1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar kasuwanci tsakanin China da Faransa

Salissou Boukari
January 9, 2018

Sakamakon wata ziyara da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ke yi a kasar China, kasashen biyu sun sanar da rattaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyin kasuwanci.

https://p.dw.com/p/2qZTt
China Staatsbesuch Emmanuel Macron, Präsident Frankreich | Xi Jinping
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, da takwaransa na Sin Xi JinpingHoto: Reuters/L. Marin

Kasar Chaina da kamfanin hako ma'adinai na kasar Faransa na Areva sun kulla yarjejeniya ta buda wata cibiyar aikata baraguzzan kayayakin makamashin nukiliya da aka riga aka yi amfani da su a kasar ta China. Kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyin kasuwanci a babban zauren shawara na Palais du Peuple tare da halartar shugaba Macron na Faransa da kuma takwaransa na kasar ta China Xi Jinping.

Ana saran jarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasar ta China da kamfanin kasar ta Faransa na Areva da ke fuskantar tarin matsaloli za ta kai ta kudi Euro miliyan dubu 10.