1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iftila'in guguwar Idai ya dauki hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
March 22, 2019

Mahaukaciyar guguwar Idai hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ta afka a kasashe uku na kudancin Afirka ta haddasa mummunan barna da asarar rayuka.

https://p.dw.com/p/3FVG0
Rettungseinsätze nach Wirbelsturm «Idai»
Hoto: picture-alliance/AP/T. Mukwazhi

A labarin da ta buga dangane da guguwar da aka yi wa lakabi da Idai jaridar Die Tageszeitung ta ce guguwar hadi da ambaliyar ruwa da suka ratsa kasashen Malawi da Mozambik da kuma Zimbabuwe sun janyo asarar dubban rayuka baya ga mummunar barnar da suka yi a kasashen uku da ke yankin Kudu maso gabashin Afirka. A kasar Mozambik guguwar ta Idai ta yi kaca-kaca da birnin Beira, daruruwan mutane sun mutu sannan wasu dubbai sun bata kana wadanda suka tsira da ransu sun yi asarar dukkan abin da suka mallaka. Jaridar ta kara da cewa ana matukar bukatar kayyakin agajin gaggawa a kasashen uku da ke jerin kasashen da suka fi fama da matsalar talauci a yankin.

Guguwar Idai da radadin sauyin yanayi.

Mosambik Buzi Nach Zyklon IDAI
Guguwar Idai ta tagaiyar mutane a MozambikHoto: Getty Images/AFP/A. Barbier

A sharhin da ta yi kan masifar guguwar ta Idai, jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa nitsewar talakawa sannan sai ta ci gaba da cewa guguwa da ambaliyar ruwa a Kudu maso Gabashin Afirka bala'i ne daga Indallahi, amma kuma ya nuna cewa wadanda ba sa taka wata rawa sosai na aikace-aikacen da ke haddasa sauyin yanayi, su suka fi jin radadin sauyin na yanayi. Jaridar ta ce guguwar Idai ta janyo ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 20 a Kudu maso Gabashin Afirka, tana mai cewa mutum kimanin miliyan biyu a kasashen Mozambik da Zimbabuwe da kuma Malawi wannan bala'i ya shafa. Ta ce alkalumma sun nuna cewa iskar da ke gurbata yanayi da dan Mozambik ko Malawi ko Zimbabuwe ke fitarwa ko kadan ba ta kama kafar wadda dan nahiyar Turai ko Amirka ke fitarwa ba, amma kuma 'yan Afirka ne suka fi jin radadin tasirin sauyin yanayin.

Yaki da cutar Ebola a Kwango

Mosambik Zyklon Idai | Zerstörung und Hilfe
Ta'adin ambaliyar ruwa a kasar MozambikHoto: Reuters/S. Sibeko

Idan kwayar cuta ta Virus ta bijire wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Zeit ta buga tana mai mayar da hankalin da cutar Ebola da ke yaduwa a kasar Kwango. Ta ce tun watan Agustan bara zuwa yau daruruwan mutane sun mutu sakamakon cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ana kuma kwatanta barkewar cutar da zama ta biyu mafi muni a cikin tarihi bayan da tsakanin 2013 da 2016 mutane dubu 11 cutar ta yi sanadin mutuwarsu a Yammacin Afirka. Jaridar ta ce akwai wahalar yaki da kwayoyin cutar a Kwango domin al'ummar yankin ba su yarda da ma'aikatan kiwon lafiya ba, musamman saboda jita-jita da ake yadawa ta kafafan sada zumunta cewa ma'aikatan na cire wasu bangarorin jikin mamata, ko ana lalata da masu neman aiki a cibiyoyin kula da masu cutar. Lamarin ya sa al'umma ke kaurace wa cibiyoyin. Amma yanzu ma'akatan kiwon lafiya na amfani da kafar sadarwa ta WhatsApp wajen dakile wannan jita-jita a kokarin kawo sauyi na halin da ake ciki