1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ina aka kwana a yaki da Boko Haram?

Katrin Gänsler/Usman Shehu Usman/PAWJune 2, 2015

Na tsawon makwanni yanzu, ake labarin nasarar da sojojin Najeriya suka yi a yaki da kungiyar Boko Haram, amma har yanzu ana samun hare-hare.

https://p.dw.com/p/1Fao7
Nigeria Selbstmordanschlag in Damaturu ARCHIV
Hoto: picture alliance/AP Photo/A. Adamu

A jawabin bayan rantsuwar kama aiki, sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya lashi takobin ganin bayan kungiyar inda ya bayyana sabbin matakai da zai bi don cimma buri.

Daga cikin sabbin matakan da shugaba Buhari ya sanar zai dauka a yaki da Boko Haram har da yi wa su kansu jami'an tsaro kwaskwarima a yakin da suke yi da Boko Haram.

Na farko dai za maida shelkwatar yaki da Boko Haram Maiduguri ba kamar yanzu ba, yadda komai sai daga Abuja ake yinsa, haka kuma Buhari a hukumance ya ce shugaban Boko Haram na Farko Muhammad Yusuf 'yan sanda suka yi ajalinsa abind a hukumomin baya suka yi ta kauce wa, duk cewa duniya na da shaidar hakan.

Nigeria Soldaten Offensive gegen Boko Haram
Za'a kwaskware yanayin aikin sojojiHoto: Reuters/J. Penney

Akwai "kanzon kurege" a batun yaki da Boko Haram

A wannan karon abun da ake ganin kamar za a samu bisa yaki da kungiyar Boko Haram shugaba Buhari ya bayyyana cewa dole sojojin Najeriya su zama masu mutunta hakkin jama'a yayin gudanar da yaki da yan ta'adda. Don haka a cewar shugaban al'ummar Chibok Tsambido Hosea Abana, shi kam bisa binciken ma da ya yi, akwai kanzon kurege ko da nasasar da ake cewa ana samu.

"A binciken da na yi na gano cewa sojojin Najeriya har yanzu basu kai ga shiga aininhin cikin dajin Sambisa. Har yanzu suna kewayen dajin ne. Don haka na yi imanin yaran suna tsakiyan dajinne. Wata kila kuma an boyu yan matanne a tsaunin Mandara dake kan iyakar Najeriya da kamaru, wannan waje ne da ake iya buya"

Ba da tsinin bindiga kadai za a kawar da Boko Haram ba

Ita kuwa Sieja Sturies, babbar jami'ar gidauniyar Frederich Ebert a Najeriya, karin haske, ta yi kan cewa ba da tsinin bindiga ne kawai za iya kawar da Boko Haram ba, sai an hada da wasu matakai.

Nigeria, Entführte Mädchen Boko Haram #BringBackOurGirls
Har yanzu ana cigiyar 'yan matan ChibokHoto: DW/Katrin Gänsler

"Boko Haram na daukar mayakansu a yankunan da hukumomi suka yi watsi da su. A yankinda kusan babu wasu ababen more rayuwa da hukuma ta gina. Idan ba hukumomi sun dau gyara zahiri ba, to gaskiya magance Boko Haram zai yi wuya"

Yanzu babban aiki ya rataya a wuyar sabbin hukumomin Najeriya, inda tuni shugaba Buhari ya ce sake gina wuraren da aka lalata da maida 'yan gudun hijira gidajensu shi ne gaban gwamnatinsa, kuma sai zaman lafiya ya samu kafin a ambaci batun komawa gida. Yanzu kuma duniya da cikin gidan Najeriya an zuba ido don gani a kasa bisa alkawuran da aka yi bisa kawar da boko Haramun.