1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na son sanin matsayar Birtaniya

Abdul-raheem Hassan MNA
March 16, 2019

Shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun ce idan aka sake yin watsi da bukatar Theresa May na ficewar Birtaniya daga EU, wajibi a samar da shiri na zahiri nan gaba.

https://p.dw.com/p/3FAUC
England, London: Theresa May
Hoto: picture-alliance/House of Commons

A wani batu mai kama da tsakiyar da ba ruwa ga firaministar Birtaniya Theresa May, shugabannin kungiyar Tarayyar Turai sun bukaci sanin inda Birtaniya ta dosa kamin su yanke shawarar daga mata kafa na ficewa daga kungiyar.

Mrs May na cikin tsaka mai wuya ganin yadda kudirinta kan matsayar kasar bayan ficewa daga EU ya gaza samun nasara a majalisar dokokin kasar.

A ranar 29 ga wannan wata na Maris aka shirya ficewar Birtaniya daga kungiyar EU a  hukumance idan har shugabannin kungiyar ba su tsawaita wa'adin ficewar ba, batun da zai mamaye taron kungiyar a mako mai zuwa a Brussels. Birtaniya na fatan tsawaita ficewarta daga kungiyar zuwa watan Yuni bayan da ta shafe shekaru biyu tana kokarin cimma matsaya.