Indiya: Gurbatatar barasa ta kashe sama da mutane 100

Mutane akalla 116 aka ba da rahoton cewar sun mutu a Jihar Uttar Pradesh da ke a arewacin Indiya, ya yin da wasu da dama suke kwance a asibiti suna yin jinya saboda amfani da gurbatatar barasa.

Yawancin wadanda suka mutu sun cikka ne a karshen mako bayan da suka sha barasar suka yi tilip. 'Yan sanda sun ce sun kama wasu wadanda ake zargi da laifin sarafa barasar har mutu kusan dubu uku.

Rahotanni masu dangantaka