1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta tsaida kasuwanci da Pakistan

Gazali Abdou Tasawa MNA
April 19, 2019

Kasar Indiya ta sanar da katse huldar kasuwancin da ke gudana tsakaninta da makobciyarta ta Pakistan ta kan iyaka da yankin Kashmir wanda kasashen biyu ke rikici kansa.

https://p.dw.com/p/3H5bF
Pakistan Auslieferung des Pilots Abhinandan Varthaman nach Indien
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K.M. Chaudary

Gwamnatin kasar Indiya dai na zargin hukumomin sojin kasar Pakistan da yin amfani da yankin Kashmir wajen safarar makamai da hodar ibilis da kuma kudin jabu.

Ministan cikin gida na kasar ta Indiya wanda ya sanar da daukar matakin ya ce za su ba da izinin komawa huldar kasuwancin kasashen biyu a wannan yanki a nan gaba bayan gwamnati ta kafa wani tsarin bincike mafi inganci. 

A shekara ta 2008 ne a wani yinkuri na kyautata huldarsu kasashen biyu wadanda sau uku suna gwabza yaki, biyu kan batun yankin na Kashmir tun bayan samun 'yancin kansu suka cimma yarjejeniyar yin amfani da wannan yanki wajen safarar kayan abinci da na marmari zuwa kasashen juna.

 A watan Fabrerun da ya gabata ma dai sun kai wa juna hari ta sama biyo bayan wani harin kunar bakin wake da ya halaka jami'an tsaron kasar ta Indiya guda 40.