Indonesia ba ta ji dadin matakin da Denmark ta dauka ba
February 12, 2006Gwamnatin Indonesia ta soki matakin da Denmark ta dauka na janye jami´anta na diplomasiya da kuma ma´aikatan ofishin jakadancinta daga birnin Jakarta bayan zanga-zangar da musulmi suka yi don nuna fushinsu da zane-zanen batanci ga Annabi Mohammad SAW da wata jaridar Denmark din ta buga. Ma´aikatar harkokin wajen Denmark ta kuma gargadi ´yan kasar da su gaggauta ficewa daga Indonesia saboda dalilai na tsaro da kuma barazana da suke fuskanta a wannan kasa. Ministan harkokin wajen Indonesia Hassan Wirajuda ya bayyana wannan mataki da cewa riga malam masallaci ne kuma babu wani kwakkwaran dalili da zai sa Denmark ta janye jami´an diplomasiyarta. Kasar dai ta kuma janye jakadunta daga Syria da Iran. Har wayau dai ana ci-gaba da gudanar da zanga-zangar yin tir da cin mutuncin al´umar musulmin, inda a jiya aka gudanar da jerin zanga-zanga a biranen London, Paris da kuma Düsseldorf.