1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi kulawa da mata 'yan gudun hijira

Ramatu Garba Baba
May 21, 2019

Kungiyar International Crisis Group ta ja hankalin gwamnatin Najeriya da ta duba halin da mata 'yan gudun hijirar Boko Haram da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar ke ciki maimakon yakar mayakan da karfin soja.

https://p.dw.com/p/3Iq9I
Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Akwai yiwuwar matan da aka ceto da kuma mazajensu suke ci gaba da yi wa Boko Haram yaki, su nemi komawa hannun mazajensu a sanadiyar hali na kunci da suka tsinci kai a sansanonin da aka tsugunar da su, ganin yadda suke fuskanta cin zarafi da yi musu fyade. 

Kungiyar ta ce muddun aka kau da kai, matsalar za ta iya haifar da wasu sabin matsaloli da ka iya dagula lissafi a kokarin da ake na ganin bayan rikicin Boko Haram.  Rahotanni na baya-bayan nan, sun nunar da cewa,  mata da kananan yara suna cikin hali na tagayyara a sansanonin da ake tsugune da su a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Abin da masana suka ce ya na tattare da hadura mara misaltuwa.