1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Inganta sana'ar wanki da guga tsakanin matasa

Kamaluddeen Sani Shawai
November 7, 2018

Wani matashi mai suna Auwal Muhammad ya bude gidan wanki da guda irin na zamani a birnin Abuja na Najeriya.

https://p.dw.com/p/37pGu
Wäscheklammern und Wäsche
Hoto: picture-alliance/blickwinkel/G. Czepluch

A sakamakon irin yadda yanzu haka a Najeriya matasa ke ci gaba da rungumar sana'oi daban-daban don kauce wa aikin gwamnati sakamakon karancin sa ya sanya wani matashi mai suna Auwal Muhammad ya bude gidan wanki da guda irin na zamani mai suna PIMAZS LAUNDRY AND DRY CLEANINGS SERVICES a fafutukar neman makoma ta gari.

Ba dai sabon labari ba ne shiga harkokin sana'ar wanki da guga a Najeriya a inda matsakaita da dattawa ke gudanar da harkar domin tsayawa da kafafun su gami da samarwa sauran matasa ayyuka wanda akasari wadanda ba su je makarantun boko ba ne ke yin ta a shekarun baya to amma ya zuwa yanzu matasa da ke da karatu mai zurfi sun fara waiwayar harkar tare da zamanantar da ita don samun makoma mai kyau a rayuwarsu.


Auwal Muhammad matashi ne daya rungumi harkar sana'ar wanki da guga a zamanance. Ibarhim Muhammed na daya daga cikin matasan da ke aiki a a gidan wankin PMAZS. Duk yake Auwal Muhammad yana fama da matsalar hasken wutar lantari amma hakan bai karya masa gwiwa a inda ya yanke shawar siyan injin don gudanar da harkokin sa ba tare da samun matsala ba daga abokan hudarsa.

Tuni dai Auwal Muhammad mai gidan wankin PMAZS ya ce yana fata nan gaba shi ne ya zama gagara misali a harkar wanki da guga a tsakanin masu irin wannan sana'ar a Najeriya.