1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraƙi ta fuskanci jerin hare-hare

November 28, 2012

A ƙasar Iraƙi aƙalla mutane 26 sun rasu sannan sama da 70 sun jikata a cikin jerin hare-haren da aka kai a kan jami'an tsaro da farar hula.

https://p.dw.com/p/16qwW
Hoto: Reuters

Masallatan 'yan shi'a guda uku da ke a Bagadaza babban birnin ƙasar ta Iraƙi ne aka nufata da hare-haren da aka ƙaddamar da yammacin ranar Talata. Jim kaɗan bayan da rana ta fadi ne aka fuskanci tashin bama-bamai da suka halaka mutane 21. A daidai wannan lokaci ne kuma aka fuskanci tashin bama-bamai a garin Kurdawa na Kirkuk da kewayensa da ke arewacin ƙasar, inda aƙalla mutane biyar suka rigamu gidan gaskiya. Waɗannan hare-hare sun auku ne a daidai lokacin da ake bukin Ashura da 'yan shi'a ke ɗauka da muhimmancin gaske. Kamar yadda aka saba 'yan ƙungiyar Alƙa'ida da sauran ƙungiyoyi masu matsanancin ra'ayi na Islama ne aka ɗora wa alhakin kai waɗannan hare haren.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal