Iraki: Kurdawa na zaben neman ballewa

A yau ne Kuradawan Iraki ke kada kuri'a a zaben raba gardama da zai basu damar ballewa daga gwamnatin Iraki, zaben dai ba shi da tasiri na cimma samun 'yancin cin gashin kai a mastayin yankin Kurdawa zalla.

Kawo yanzu dai wannan zabe na ci gaba da haifar da fargabar ga makomar zaman lafiya a yankunan da suka sha fama da masu tada kayar bayan kungiyar IS. A nasu bangaren gwamnatin Turkiyya, ta dauki matakan soji na toshe kan iyakar ta da yankunan Kurdawan a yunkurin nuna rashin goyon bayan zaben neman ballewar. Wannan ya sa Firaiminstan Iraki Haider al-Abadi, ya yi kakkausar suka ga matakin Kurdawan na neman raba kasa.

"Ba za mu yi watsi da al'ummar Kuradawa ba, mun yi watsi da shirin samar da yanki mai wariya. Iraki za ta ci gaba da kasancewa ta al'ummar Iraki, ba za mu amincewa kowa ya taka doka ba."

 

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka