1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta nemi goyon bayan Rasha a yaki da IS

Salissou BoukariMay 21, 2015

Firaministan Iraki Haider Al-Abadi da ke wata ziyara a Rasha, ya yi kira da ta bada himma wajen yaki da kungiyar IS wadda ke mamaye da wasu sabin wurare a Iraki.

https://p.dw.com/p/1FTnR
Haider Al Abadi
Haider Al AbadiHoto: picture-alliance/dpa

Firaministan na Iraki ya yi wadannan kalammai ne yayin tattaunawarsa da takwaransa na Rasha Dimitri Medvedev, inda ya ce ayyukan 'yan ta'addan na kara karfi tare kuma da daukar wani sabon salo.

Al-Abadi ya sanar da mahimmancin huldar kasarsa da Rasha a wannan lokaci, inda ya ce kuma wannan ziyara tashi ta tattabar da haka. Daga nashi bangare takwaransa na Rasha Dimitri Medvedev, ya yaba wannan ziyara, wadda ita ce ta farko tun lokaci da ya hau kan wannan mukami. Daga bisani Firaministan na Iraki zai gana da Shugaban Rasha Vladimir Putine.