1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da MDD a kan rikicin nukiliya

March 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3a

Manyan kasashe masu fada a ji sun yi kira ga kasar Iran ta martaba bukatar da majalisar dinkin duniya ta yi mata na dakatar da shirin ta na makamashin Nukiliya ko kuma a mayar da ita saniyar ware. Kasar Britaniya ta yi kashedin cewa Iran za ta fuskanci takunkumin majalisar dinkin duniya idan ta ki dakatar da sarrafa sinadarin Uranium wandanda a ke zargi za ta iya kera makamai da su. A waje guda shugaban hukumar makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya Mohammed el-Baradei ya bukaci yin taka tsantsan wajen sanyawa Iran takunkumi, yana mai cewa yin hakan ba zai zamanto mai alfanu ba, domin a halin da ake ciki Iran bata nuna wata barazana mai tada hankali ba. Sai dai kuma el-Baradei ya ja hankalin Iran da kosawar kasashen duniya a game da batun nukiliyar, inda ya bukace ta da ta hanzarta mika masa bayanai a game da shirin ta na nukiliya. Iran wadda ta ce shirin ta na nukiliya na lumana ne ta yi fatali da kudirin da kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya zartar na waádin kwanaki 30 ta dakatar da shirin nukiliyar baki dayan sa.