1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta kai ga matakin kusa ga na karshe a yunƙurinta na sarrafa uranium

October 25, 2012

Nan ba da jimawa ba ƙasar Iran za ta kai ga sarrafa uranium a yunƙurin da ta ke yi na sarrafa wannan ƙarfe.

https://p.dw.com/p/16XAd
Produkte aus der nuklearen Forschungsanlage in Teheran Quelle: aeoi.org.ir (Abkürzung für die Webseite Atom Energy Organisation Iran)
Hoto: aeoi.org.ir

Bisa ga dukkan alamu, ƙasar Iran ta cimma wani matsayi a matakinta na kaiwa ga sarrafa sinadarin uranium. Wannan kuma shi ne wani sakamakon binciken da ofisoshin wasu jakadan kasashen wajen suka ce sun samu. Wasu rahotanin sun bayana cewar a yanzu kam,kasar ta Iran ta samu kafa wasu na'urorin da suka rage mata gurin ci-gaba da sarrafa sinadarin wanda kasashen yammaci suka zargi ƙasar da yunkurin ƙera makaman nukleya zargin da hukumomin kasar suka yi watsi da shi. Kasar dai ta nace ne a kan duk wani yunkurin da ta yi a dangane da batu,na samarwa jama'an kasar wutar lantarki ne da kuma sha'anin kiyon lafiya. Kawo yanzu dai hukumar kulla da makamashi ta duniya bata ce komai ba akan wadanan sabbin bayanan wadanda kan iya haddasa gaugauta kaiwa kasar hari kamar yada Isra'ila ke barazana.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal