1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tayi kunnen uwar shegu da umarnin kungiyyar Eu

January 9, 2006
https://p.dw.com/p/BvD1

Mahukuntan kasar Iran sun sanar da ci gaba da gudanar da bincike na musanman dake da nasaba da makamin nukiliya a wannan rana ta litinin.

Wannan dai sabon mataki da kasar ta dauka da alama ka iya kara dumama yanayin danganta dake tsakanin kasar da kasashen yamma, bisa la´akari da irin matsin lambar da suke mata na watsi da aniyar mallakar makamin na nukiliya.

A can baya dai kungiyyar gamayyar turai wato Eu ta gargadi kasar da kada ta ci gaba da sarrafa sanadarin ta na Uranium, to amma kuma kasar ta Iran tace tana da yancin ci gaba da hakan domin nukiliyar ta ta habaka wutar lantarki ce, amma bata tashin hankali ba.

Bisa dai wannan sabon mataki da kasar ta Iran ta dauka, ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier cewa yayi alama ce ta kunnen uwar shegu da kasar ke son nunawa, wanda hakan ka iya janyo mata hukunci da zata yi kuka dashi.

A wani lokaci ne a cikin wannan makon, ministan yace zai tattauna da takwarorin sa na Biritaniya da Faransa don sanin matakin daya kamata.