1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran zata halarci taron tabbatar da tsaro a Iraƙi

March 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuQF

Iran ta sanar da cewa zata halarci gun taro kan harkokin tsaro a birnin Bagadaza wanda zai gudana a ranar asabar, wanda kuma jami´an Amirka zasu halarta. Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Mottaqi yaa ba da wannan sanarwa a gun wani taron manema labarai a birnin Teheran. Ya ce tawagar Iran zata halarci taron don taimakawa gwamnatin Iraqi da kuma kasar ta Iraqi. Taron zai ba da damar zama kan teburin shawarwari daya tsakanin jami´an Iran da na Amirka. Da farko wakilin Amirka a taron Zalmay Khalilzad ya ce ba bu wani shiri na tattaunawa ido da ido da Iran, to amma a shirye ya ke ya tattauna game da zargin da aka yi cewa ana amfani da makaman Iran akan dakarun Amirka a Iraqi.