1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta Tilastawa mutane dubu 3,500 ayyukan bauta

Kamaluddeen SaniJanuary 19, 2016

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta futar da wani rahoto a yau dake nuni da cewar kungiyar IS ta tilastawa kimanin mutane 3,500 shiga ayyukan bauta musamman mata da kana nan yara.

https://p.dw.com/p/1HgAw
IS Kolonne Fahrzeuge Toyota
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A yayin da take karin haske kan rahoton mai magana da yawun hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya Ravina Shamdasani ta kara da cewar,

Masifar da mutanen Iraki suke fuskanta tana da yawa,kungiyar IS na yin garkuwa da kana nan yara gami da san yasu cikin kungiyar dake a gaba- gaba wajen tinkarar yaki,kuma duk wanda ya gudu saboda razana da zarar an kamo shi sai a yanke masa hukunci,mata an tilas ta musu shiga ayyukan lalata.

Kungiyar IS wacce ta mamaye mafi yawacin arewaci da yammacin Iraki a shekara ta 2014 wadda kuma har yazu take da ikon a mafi yankunan Iraki da Syriya na cigaba da haifar da barazanar zaman lafiya a duniya baki daya.