1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isira'ila ta kai sabbin hare hare a Gaza

November 17, 2012

Dakarun Isira'ila sun yi kaca kaca da fadar gwamnatin Hamas a rana ta fuɗu ta faɗan da suke gwabzawa da mayaƙan ƙungiyar Hamas

https://p.dw.com/p/16kpN
A Palestinian searches for victims under the rubble of the destroyed house of a Hamas official after an Israeli air strike in Jabalya in the northern Gaza Strip November 17, 2012. REUTERS/Mohammed Salem (GAZA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS)
Hoto: Reuters

Sojojin Isira'ila sun kai wasu sabbin hare hare na rokoki ta jiragen saman yaƙi a kan fadar gwamnatin Hamas da ke a yankin Zirin  Gaza a ranar ta fuɗu a faɗan dake ƙara yin muni tsakanin sasan biyu.

Masu aiko da rahotanin sun ce jiragen yaƙi na Isira'ila sun yi wa cibiyar gwamnatin Hamas ɗin kaca kaca tare da lallata wasu gidajan jama'ar da ke kusa da fadar.Wani wanda ya ganewa idon sa abinda ya faru ya ce babu abinda ya yi sauran a ofishin.

A ƙalla falasɗiniyawa guda tallatin ne suka rasa rayukan su a ƙwanaki fuɗu na faɗa yayin da wasu 280 suka jikata.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita       : Umaru Aliyu