1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ISIS ta ayyana kafa kasar Musulunci

June 30, 2014

Kungiyar 'yan tawayen ISIS dake da nasaba da al-Qaida ta ayyana kafa sabuwar Jamhuriyar Mususlunci tare da neman goyon bayan Musulmi.

https://p.dw.com/p/1CSXB
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kungiyar dai a yanzu haka ta samu nasarar kwace mafiya yawan yankunan dake arewa maso gabashin Siriya da kuma da yawa daga cikin yankunan dake kasar Iraqi. Masu tsattsauran ra'ayin dai sun samu nasarara rushe kan iyakar kasashen Iraqin da Siriya inda kuma a nan ne suka ayyana kafa sabuwar Jamhuriyar Musuluncin tare da bayyana shugaban kungiyar ISIL Abu Bakr al-Baghdadi a matsayin shugabanta. Rahotanni sun bayyana cewa sun kuma ayyana haramta dukkan masarautu da sauran gwamnatoci dake kasashen Musulmi tare da yin kira ga Musulmin duniya baki daya da suyi mubaya'a ga Abu Bakr al-Baghdadi a matsayin sabon Khalifa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar