1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Hamas sun amince da tsagaita wuta.

August 1, 2014

A karo na farko tun bayan soma rikicin Isra'ila da Hamas, bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta na tsawon kwanaki uku daga wannan Juma'a (01.08.2014).

https://p.dw.com/p/1CnEo
Symbolbild Palästina Israel Flaggen Konflikt
Hoto: picture-alliance/dpa

Hakan na zuwa ne bayan da yankin na Gaza ya shafe awoyi 24 a baya, yana fuskantar ruwan bama-bamai mafi muni da ya haddasa rasuwar mutane masu yawan gaske. Sai dai kuma kara gayyato sojoji dubu16 da Isra'ilan ta yi, da kuma aniyarta na ci gaba da rusa hanyoyin karkashin kasa da ke yankin a lokacin tsagaita wutar, na barazana ga batun na tsagaita wuta, domin kuwa Kungiyar Hamas ta ce zata maida martani ga duk wani aikin soja da Isra'ilan zata yi tsawon lokacin tsagaita wutar.

A daura da haka, tawagogin Isra'ilan da Falasdinawan, na shirin fara tattaunawar kai tsaye a Masar, don cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai dorewa. A kalla cikin wannan lokaci na tsagaita wuta, Falestinawa milian daya da 800 ne zasu samu agaji na abinci daga kungiyoyin kasa da kasa, tare da samun damar bizne mutanan da suka rasu, da aiwatar da sauran bukatun su na gagawa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar