1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai sabon hari da rokoki a Isra'ila

Abdul-raheem Hassan
March 25, 2019

'Yan sanda sun tabbatar da harin rokoki da ya jikkata akalla mutane biyar a yankin Mishmerat mai tazarar mita 50 da yankin zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/3FbS3
Israel Haus von Rakete getroffen
Hoto: Reuters/Y. Sagi

Mazauna yankunan arewacin birnin Tel Aviv sun bayyana yadda karar harbe-harben bindigogi da ababen fashewa suka tashesu daga bacci, amma sojojin Isra'ilal na zargin Falasdinawa da haddasa gobara bayan harba rokoki da suka fashe kan wani gida a garin Mishmerat.

Akwai fargabar Isra'ila za ta maida martani kan sabon harin, inda firaiministan kasar Benjamin Netanyahu da ke ziyara a kasar Amirka ya sanar da shirinsa na katse ziyararsa in ya gama da Shugaba Trump zuwa jimawa don komawa Isra'ila din da nufin tinkarar batun.

Sake barkewar rikici tsakanin Faladsinawa da Isra'ila na jefa faregaba ga makomar zaben Isra'ilan da zai gudana a ranar 9 ga watan gobe, zaben da ake ganin Netanyahu na fuskantar kalubale daga 'yan adawa kan zargin cin hanci.