1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila na yin barin wuta a Gaza

July 9, 2014

Sojojin kasar Isra'ila sun ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankin Zirin Gaza na Palasdinu a rana ta biyu a jere.

https://p.dw.com/p/1CZ5F
Hoto: picture-alliance/dpa

Akallah Palasdinawa 44 ne suka rasa rayukansu sakamakon barin wutar da jiragen yakin Isra'ilan ke ci gaba da yi ta sama a Zirin na Gaza. Hukumomin Palasdinun sun ce akallah fararen hula 38 da suka hadar da kanan yara 10 na daga cikin Palasdinawa 44 da suka rasa rayukansu cikin kwanaki biyu na hare-haren da sojojin Isra'ilan ke kaiwa. Rahotanni sun tabbatar da cewa kimanin 300 kuma sun samu munanan raunuka baya ga wadanda suka kauracewa gidajensu ala tilas domin tsira da rayukansu. Isra'ilan dai ta yi ikirarin cewa ta na kai hare-haren ne domin yin maganin Palasdinawan da ke kai mata hari ta hanyar jefa mata rokoki. Hare-haren na baya-bayan nan dai na zaman wani gagarumin fada a tsakanin bangarorin biyu tun bayan na tsahon kwanaki takwas din da suka fafata a watan Nuwambar shekara ta 2012. Isra'ila dai ta jibge sojojinta masu yawa a kan iyakarta da Zirin Gaza wanda ke karkashin ikon 'yan kungiyar Hamas ta Palasdinawa a wani yunkuri na afka musu ta kasa baya ga hare-haren da ta ke kaiwa ta sama, sai dai suma a hannu guda suna ci gaba da kai hari da makaman roka zuwa Isra'ilan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba