1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ISWAP tayi garkuwa da ma'aikatan gwamnatin Borno

Ramatu Garba Baba
December 2, 2021

Ana kyautata zaton mayakan Kungiyar ISWAP ne suka yi garkuwa da ma'aikatan gwamnatin jahar Borno shida daga yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/43kNO
Nigeria Baga | Truck des IS Gruppe (ISWAP)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun hallaka wasu mayakan ISWAP da Boko Haram da dama a jihohin Borno da Yobe. Harin na ranar Larabar da ta gabata, ta rutsa da ma’aikatan guda shida ne a kan hanyar da ake yi a tsakanin garuruwan Damboa da Chibok da ke fama da matsalolin tsaro.

Ya zuwa yanzu babu labarin inda aka kai wadannan ma’aikata ko kuma halin da suke ciki inda iyalai da ‘yan uwa da abokan arziki suka fada cikin tashin hankali. Gwamnatin jahar Borno ta bakin kwamishinan aiyuka na jahar Yerima Saleh ta tabbatar da labarin kame jami’an guda shida da wasu motoci mallakar gwamnatin guda biyar da suka sace.

Karin BayaniISWAP ta sako ma'aikatan agaji da ta kama

Nigeria Borno State Maiduguri | Angehörige von entführten Entwicklungshelfern
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Kokarin ji daga bakin iyalan wadannan ma’aikata wanda yanzu ke cikin tsananin tashin hankali ya ci tura. Wani abu da kame ma’aikatan ya fito da shi, shi ne karuwar tabarbarewar tsaro  musamman a yankuna kudancin jahar Borno inda kusan a kullum sai an samu rahoton kai hari ko dai kan jami’an tsaro ko kuma fararen hula matafiya.

A bangaren daya kuma sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram da ISWAP da dama bayan wasu jerin hare-hare da suka kai a Gajiram a jahar Borno da kuma Buni Yadi a jihar Yobe. Baya ga Sojojin da suka aiyana nasarar hakan al’ummar da ke yankuna ma sun tabbatar da samun wannan nasarar.

Karin Bayani: Najeriya ta tabbatar da kisan al-Barnawi

Yayin da ake fuskantar karuwar tafiye-tafiye a wannan watan na Disamba a saboda bukukuwan da aka sa a gaba, mutane na baiyana damuwa saboda yadda hanyoyi a jahohin Arewa maso Gabashin Najeriya suka zama tarkon na mayakan Boko Haram da ISWAP da ke fitowa suna kame mutane don yin garkuwa da su.