1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da laluben gawarwaki a cikin Tekun Bahar Rum

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 7, 2015

Italiya ta sanar da cewa ta samu nasarar gano barakuzan jirgin ruwan da ta hakikance shine wanda ya yi hadari a Teku cikin watan Afirilun da ya gabata.

https://p.dw.com/p/1FMWD
Gawarwakin bakin hauren da suka mutu a Tekun Bahar Rum
Gawarwakin bakin hauren da suka mutu a Tekun Bahar RumHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Buccarello

Hadarin dai ya yi sandiyar hallaka mutane kusan 900 da suka taso daga Libiya a kokarinsu na shigowa nahiyar Turai. A ranar 18 ga watan na Afirilu ne hadarin da aka bayyana da mafi muni a Tekun na Bahar Rum ya afku, inda kawo yanzu aka samu nasarar gano gawarwaki 24 kacal daga cikin daruruwan mutanen da suka rasa rayukansu. Gano barakuzan jirgin da aka yi a can karkashin Tekun kimanin tazarar kilomita 84 zuwa kasar Libiya na sanya sabon fata na yiwuwar kara gano gawarwakin mutanen. An dai samu nasarar ceto mutane 28 daga cikin bakin hauren da ke cikin wannan jirgi wanda ke makare da bakin haure. Rahotanni na nuni da cewa akallah mutane 1,800 ne suka nutse a Tekun na Bahar Rum a wannan shekara ta 2015 da muke ciki, duk dai a kokarinsu na tsallakowa Turai da suke wa kallon "Tudun mun tsira".