1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ja-in-jar sojoji da gwamnati a Cote d'ivoire

May 15, 2017

Sojojin Cote d'ivoire sun sake yunkurowa don ganin sun kawo karshen tashin hankalin da ya biyo bayan boren da sojoji ke yi don tilastawa gwamnati biyansu wasu hakkoki nasu.

https://p.dw.com/p/2d0w0
Elfenbeinküste Soldatenmeuterei
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Mutane fiye da 10 ne suka sami rauni a tsawon kwanakin hudu da sojojin suka kwashe suna ja-in-ja da gwamnati, ya zuwa yanzu dai tsofaffin 'yan tawayen da suka koma aikin soji sun mamaye yawancin manyan biranen kasar. Al'ummar  birnin San Pedro sun wayi gari suna jin kararrakin bindiga a ranar Litinin din nan a wannan  gari na biyu mafi girma a kasar ta Cote d'ivoire, rahotanni na kuma cewa wasu 'yan bindiga sun tsare babbar hanyar shiga kasar ta birnin Abidjan a wannan sabon rikicin da ya barke a tsakanin gwamnati da sojojin kasar da ke bore don ganin an biyasu sauran hakkokinsu kamar yadda gwamnati ta yi alkawari a baya.

Toh  a yayin da gwamnati ke ikirarin tura dakarun soji don ganin sun tabbatar da doka da oda a manyan biranen da rikicin ya fi kamari, rahotanni na nuni da cewa al'amarin  ya fa  janyo cunkoson ababen hawa tare da tsayar da hada-hadar yau da kullum, Zamble Bi kalou direban motar dakon kaya da ya kwashi tsawon kwanaki a wuri guda ya nuna takaicinsa da hakan.

Elfenbeinküste Meuternde Soldaten halten Verteidigungsminister fest
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Faduwar farashin Cocoa da kasar ke dogaro da shi a kasuwannin duniya na daga cikin dalilan da gwamnati ta bayar na kasa cikawa sojojin alkawarin biyansu sauran alawus kamar yadda ta dauki alkawarin yi a baya.

Charles Legre daya daga cikin mutanen da suka hada nasu gangamin adawa da bukatun sojojin ya na ganin ya kamata sojojin su kai zuciya nesa.

Yanzu haka dai mutane akalla takwas ne suka sami munannan rauni a tsawon kwanakin da aka kwashe ana fuskantar tirjiyar daga sojoji da suka tsaya tsayin daka don samin biyan bukata yayin da gwamnati ke kuma cewa zata yi amfani da karfi don maganace matsalar, sai dai a cewar wani tsohon jandarmar ya dai kamata a sasanta a tsakanin bangarorin biyu maimakon anfani da karfi.

Sojojin da ke wannan boren dai 'yan tawayen da suka amince su ajiye makamai ne bayan kawo karshen kazamin yakin basasa na fiye da shekaru goma a Cote d'ivoire sun kuma taka muhinmiyyar rawa wajen kafa gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara.