1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

JAMB: Rangwame ga masu bukata ta musamman

January 16, 2024

Masu bukata ta musamman a jahohin katsina da Zamfara, sun yaba matakin hukumar JAMB na yafe wa dalibai kudin takardar cikewa ta neman shiga makarantun Ilmi mai zurfi na zangon karatun 2024/2025.

https://p.dw.com/p/4bKmc
Hoto: Sumit Sanyal/picture alliance

Magatarkar hukumar ta Jamb Prof Ishaq Oloyede ya tabbatar da umarnin yi masu rigistar rubuta jarabawar kyauta a wata sanarwa, haka kuma sanarwar ta ce za'a samar wa daliban litattfan karatun da suka shafi jarabawar kuma a karantasu a nadesu a faifan murya dan raba wa bangaren makafi kyauta. Matakin hukumar yazo a lokacin da ya dace a cewar Lawal Jibril Shugaban makarantar sakatare ta masu bukata ta musamman bangaren makafi a jihar katsina

Dalibai masu bukatar ta musamman sun baiyana gamsuwa matakin wanda suka ce zai karfafa musu gwiwa.

Binciken masana ya nuna kasa da kashi goma cikin dari ne na dalibai masu bukata ta musamman ke samun damar wucewa makarantun gaba ta sakandire a jahohin Katsina da Zamfara saboda yadda kayan karatun su ke da tsada.