1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da soke hukuncin kisa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Suleiman Babayo
June 1, 2022

Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da watsi da dokar hukuncin kisa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4C8lj
ZAR Bangui Treffen Verfassungsrichter
Hoto: Nacer Talel/AA/picture alliance

Babban jami'ar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi maraba da mataki majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wajen soke dokar hukuncin kisa a kasar mai fama da tashe-tashen hankula.

Jami'ar Michelle Bachelet ta yaba tare da karfafa gwiwa ga Shugaban kasar Faustin-Archange Touadera kan ya saka hannu a kan sabuwar ayar dokar. Karo na karshe da aka zartas da hukuncin kisa a kasar tun shekarar 1981, fiye da shekaru 40 da suka gabta.

Ita dai Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kasance kasa ta 24 na kasashen Afirka da suka yi watsi da dokokin hukuncin kisa. A duniya baki daya kimanin kasashe 170 suka yi watsi da dokokin hukuncin kisa.