1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na bukatar makamai

Yusuf BalaSeptember 27, 2014

Nasarar ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a wannan kasa ta dogara ne kan tallafin da dakarun kasar za su bayar saboda haka a cire mata takunkumin makamai.

https://p.dw.com/p/1DM64
Catherine Samba-Panza
Hoto: Reuters

Shugabar kasar jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Catherine Samba-Panza ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta dage wa kasar takunkumin sayen makamai da aka sanya mata, ta yadda dakaraun sojan kasar za su sami kayan aiki su kuma tallafawa ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

A jawabin ta na farko a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya Shugaba Samba-Panza ta kuma bukaci tallafin kasa da kasa kan yadda za a bi wajen raba mayakan sakai da ke dauke da muggan makamai a kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wadanda ke ci gaba da iza wutar rikicin wannan kasa wacce ke fama da talauci tun bayan juyin mulki da aka yi a watan Maris na shekarar 2013.

Bayan da ta jaddada godiyar ta ga kasashen da suka tura dakaru cikin tawagar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a wannan kasa da ke fama da rikice-rikice ,shugaba Panza ta ce nasarar ayyukan dakarun na Majalisar Dinkin Duniya za ta dogara ne idan suka sami tallafin dakarun sojan kasar wadanda suka kware wajen sanin lunguna da sakuna na kasar su.

A watan Disambar shekarar 2013 ne dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wannan takunkumi a kan kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya bayan da rikici mai nasaba da addini ya balle a tsakanin mayakan Musulmai da Kirista.