1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamhuriyar Nijar ta yi sabuwar ministar harkokin waje

Suleiman BabayoFebruary 25, 2015

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou - ya yi wa gwamnati garanbawul

https://p.dw.com/p/1Ehr6
Hoto: DW/M. Kanta

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yi wa majalisar ministocinta wani gyaran fuska a ɗaukacin ministoci 36 da ke cikin majalisar ministocin na nan, sai dai ministan harkokin wajen ƙasar Malam Bazoum Mohamed da majalisar ta sauya tare da maye gurbinsa da Daraktar fadar Firaministan kasar Malama Aichatou Kane Boulama a yayin da shi kuwa Bazoum din aka naɗa shi a muƙamin babban minista a fadar shugaban ƙasa.

Wannan shi ne dai karo na huɗu ke nan a tarihin gwamnatin ƙasar da shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou ke yi wa gwamnatinsa gyara fuska inda mutane da dama ke yi wa gwamnatin kallon tamkar gwamnati ce ta yaƙin neman zaɓe ganin irin yadda zaɓuɓɓuka ke ƙaratowa a ƙasar.