1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamian tsaro sun harbe mutane 10,a boren dalibai a Conakry.

Zainab A MohammadJune 13, 2006
https://p.dw.com/p/Btzk
Jamian tsaro da Dalibai a Conakry,Guinea.
Jamian tsaro da Dalibai a Conakry,Guinea.Hoto: AP

Gwamnatin kasar Guinea ta bayyana damuwanta ,dangane asaran rayuka da akayi sakamakon arangaman da jamian tsaro sukayi da dalibai dake zanga zanga.

Rahotanni daga wadanda suka ganewa idanunsu yadda wannan rikici ya gudana ya zuwa yanzu dai na nuni dacewa,mutane 10 ne suka rasa rayukansu,ayayinda gwamnati taki sanar da adadin mutane da suka rasa rayukansu a wannan rigima data barke a jiya litinin sakamakon soke rubuta jarrabawa da akayi,saboda yajin aikin malaman makaranta.

Rahotannin kafofin yada labaru dban daban na nuni dacewa,mutane 7 ne aka bindige har lahira a birnin conakry dake zama fadar gwamnati,ayayinda saura ukun a wani gari da ake kira Labe,mai tazarar km 400 arewacin birnin na conakry.

Akasarin wadanda suka rasa rayukan nasu dai matasa ne dalibai,wadanda dakarun gwamnati sukayi ta harbi da bindiga a yayin wannan zanga zanga na jiya.Bugu da kari mutane da dama sun jikkata,a wannan yamutsi da ahnnu guda kuma keda nasaba da yajin aikin kasa baki daya da kungiyar kwadagon Guinea mafi girma ta kira,bisa laakari da cigaban tabarbarewan tattalin arziki da rashawa dake cigaba da samun gindin zama a wannan kasa dake da dumbin albarkatun kasa.

Tun a makon daya gabata nedai gwamnatin shugaba Lansana Conte,tayi gargadin cewa zata dauki tsauraran matakai a dangane da duk wanda ya nemi tayar da hankali a yayin wannan yajin aiki na kasa baki daya daya fara ranar alhamis.

Sai dai tun wayewar garin yau talata nedai ake cigaba da arangam tsakanin dalibai da jamian tsaro na gwamnati,wadanda ke amfani da barkonon tsohuwa wajen kokarin kwantar da lamarin.

Kimanin dalibai dubu 94 nedai aska soke gudanar musu da jarrabawarsu ta karshe,ba tare da a tsayar da ranar sake rubuta jarrabawar ba.A makon daya gabatan ne kuma kungiyoyin kwadagon Guinean suka lashi takobin cewa bazasu janye yajin aikin ba,har sai an maganta musu matsalolin su.Maaikatan dai na bukatar karin albashi tare da ragin farashin man petur,wanda ya haura da kashi 30 daga cikin 100 a watan daya gabata kadai.

Kazalika,kungiyar kwadagon ta kuma koka dangane da karuwan rashawa da cin hanci ,da almubazzaranci a bangaren gwamnatin kasar ta Guinea.

Rahotanni daga conakry dai na nuni dacewa,sakamakon zanga zangar ,shugaba Lansana Conte a jiya da maraice ya gana da shugabannin kungiyoyin kwadagon da suka shirya yajin aikin,kana ya umurci ministan kasar daya biya bukatun maaikatan.

Yajin aikin kasa baik daya aGuinea,wanda ya fara tun ranar alhamis din makon daya gabata dai,ya durkusar harkokin cigaban wannan kasa dake yammacin Afrika,saboda kasancewar bankuna da wuraren kasuwanci a rufe.