1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adamawa: APC ta soki ranar sake zaben gwamna

Uwais Abubakar Idris
March 27, 2019

Yayin da hukumar zabe ta kasa a Najeriya INEC ta sanar da ranar 28 ga watan Maris domin gudanar da zabe a mazabu 44 a Jihar Adamawa na zaben gwamna da ba a kammala ba, jam'iyyar APC mai mulki ta yi watsi da ranar zaben.

https://p.dw.com/p/3FlIR
Nigeria Regionalwahlen
Hoto: Ma'awiyya Sadiq

Jamiyyar APC mai mulki a jihar Adamawa ta bayyana rashin amincewarta da ranar da hukumar zabe ta tsayar domin ci gaba da zaben gwamna a mazabu 44 na jihar.

Sakataren gudanarwa na jamiyyar Ahmed Lawan ne ya sanar da matsayin jamiyyar a Yola.

Jamiyyar ta yi watsi da ranar Alhamis 28 ga wannan watan na Maris da hukumar zaben ta sanar domin gudanar da zaben bisa hujjar cewa ba’a tuntube su ba kafin tsayar da ranar.

Hukumar zabe mai zaman Kanta ta Najeriya, INEC ta tsayar da ranar 28 ga watan Maris domin gudanar da zaben gwamnan jihar Adamawan a mazabun  44 da ke kananan hukumomi 14 na jihar.

Masu jefa kuri’a dubu 40,988 ne za su yi zaben wanda zai kai ga fitar da wanda zai yi nasara a matsayin gwamnan jihar ta Adamawa.