1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka: Sakamakon zaben fidda gwanin jam'iyyar adawa

February 5, 2020

Pete Buttigieg ya samu kuri’u mafi rinjaye a fafatawar zaben fitar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Demokrat na jihar Iowa bayan da ya yi galaba kan tsohon mataimakin Shugaban kasa Joe Biden.

https://p.dw.com/p/3XJn3
Pete Buttigieg ya samu kuri’u mafi rinjaye a zaben fitar da dan takarar shugaban kasa
Pete Buttigieg ya samu kuri’u mafi rinjaye Hoto: Getty Images/S. Platt

Bayan da aka shafe wasu sa’oi cikin rudani, daga karshe, Jam’iyar Demokrats ta fara bada wani daga cikin sakamakon zaben fitar da dan takarar a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata a jihar Iowa, a dai-dai wannan lokaci da ‘yan-takara suka karkata zuwa zaben jihar New Hampshire.

An baiyana sakamakon zaben dan takarar Shugabancin da aka gudanar a jihar Iowa
An baiyana sakamakon zaben dan takarar Shugabancin da aka gudanar a jihar IowaHoto: picture-alliance/AP/C. Neibergall

Kodayake har yanzu babu wanda aka ayyana da cewa, shi ne ya lashe zaben, amma zuwa yanzu, dan takara Pete Buttigieg, yake sahun gaba da kusan kashi 28 cikin dari na kusan kashi 80 na sakamakon da aka fitar, sai Sanata Bernie Sanders da ke biye masa da kusan kashi 26, yayin da shi kuma tsohon mataimakin Shugaba Barack Obama, watau Joe Biden yake kusan matsayi na hudu da kashi goma sha shida, duk da kyakykyawar fatar da ake yi cewa, shi ne mutumin da zai iya fafatawa da Shugaba Donald Trump sosai.

 

Ganin yadda wannan matashi mafi karancin shekaru a zaben, watau Buttigieg yake bada mamaki, duk da yake suna cigaba da yin kunnen-doki da dattijo Bernie Sanders, ana ganin cewa, komai zai iya faruwa a irin wannan zabe na share-fage, musanman ganin cewa, galibin ‘yan takara hudu da ke sahun gaba, tsaffin ‘yan siyasa ne da jama’a suka saba da jin kalamansu, don haka akwai yi yuwa hakan ne ya sa Pete Butteiege ya bada mamaki.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya zo na hudu
Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya zo na huduHoto: Getty Images/J. Sullivan

 

Tun farko da yake yin jawabi bayan fara fitar da sakamakon zaben, jagoran jamm’iyar Demokrats a jihar ta Iowa Troy Price, ya nuna takaicinsa ga kwamacalar da aka samu  wadda ta haddasa rashin samun sakamakon. A dai-dai wannan lokaci da ‘yan-takarar na Demokrats suka dunguma zuwa jihohin New Hamspshire da Nevada, an fara korafe-korafen cewa, ya kamata a dai na bai wa jihar Iowa matsayin farko na gudanar da irin wannan zabe mai mahimmanci, musanman ganin matsalolin da aka fuskanta da kuma yadda jihar ta kasance karama sosai.