1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zanga zangar nuna kyama ga matakan dakile corona

Abdoulaye Mamane Amadou
May 16, 2020

Ana sa ran duban jama'a za su fito yin zanga-zanga a wasu jihohi dabam-dabam na tarayyar Jamus don nuna rashin jin dadinsu kan matakan takaita zirga-zirga da hukumomi ke dauka don dakile Covid-19.

https://p.dw.com/p/3cKG1
Deutschland Berlin | Coronavirus | Protest
Hoto: Reuters/C. Mang

Rahotanni daga sassan kasar Jamus sun ce masu akidar tsananin kyamar baki da dama ne ake hasashen za su fito don yin zanga-zangar a karshen wannan mako ciki har da jihohin Munich da Dortmund da ma babban birnin kasar wato Berlin.

Akalla mutun dubu biyar ne suka fito yin boren a baya a birnin Stuttgart, duk da matakin hana yin duk wani taron da ke tara jama'a da hukumomin kasar suka yi a baya.

Masu boren dai na ci gaba ne da nuna kyama kan matakan gwamnatin kaar da suka kira na hana walwala da 'yan cin jama'a.