1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An kasa cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Gazali Abdou Tasawa
June 27, 2018

Taron kawancan jam'iyyun da ke mulki a Jamus da aka shirya a jiya Talata da nufin dinke barakar da aka samu tsakanin jam'iyyar CDU da abokiyarta ta CSU kan batun 'yan gudun hijira ya watse baram-baram. 

https://p.dw.com/p/30MY0
Deutschland Berlin Sitzung der CDU/CSU-Fraktion | Alexander Dobrindt & Angela Merkel
Hoto: picture alliance/dpa

A kasar Jamus taron kawancan jam'iyyun da ke mulki da aka shirya a jiya Talata da nufin dinke barakar da aka samu tsakanin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma abokiyarta ta CSU kan batun 'yan gudun hijira ya watse baram-baram. 

Bayan tattaunawa ta sama da awoyi hudu taron da ya hada jam'iyyun na CDU da CSU da abokiyar kawancensu ta SPD ya kawo karshe ba tare da cimma wata matsaya ba. Sai dai illahirin shugabannin jam'iyyun uku sun bayyana bukatar ci gaba da zama tare da kuma laluben hanyoyin fahimtar juna kan sabanin da aka samu. 

Shugaban jam'iyyar ta CSU kana ministan cikin gida na kasar ta Jamus Horst Seehofer na son daukar matakin korar daga cikin kasar ta Jamus 'yan gudun hijirar da suka rigaya suka yi rijista a wata kasar ta Turai, matakin da shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta nuna rashin amincewarta da shi.