1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An yi jana'izar Helmut Kohl

Ahmed Salisu
July 1, 2017

A ranar Asabar ce (01.07.2017) aka yi jana'izar tsohon shugaban Jamus Helmut Kohl da ya rasu cikin watan jiya. Kafin a binne shi an yi wani zama don girmama shi a majalisar dokokin EU da ke birnin Strabourg na Faransa.

https://p.dw.com/p/2flsB
Trauerfeierlichkeiten für Altkanzler Kohl
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Arnold

Tun da misalin karfe goma na safiyar Asabar ce shugabannin Turai da na sauran kasashen duniya suka fara hallara a zaune majalisar dokoki na kungiyar EU inda daga bisani aka sanya kawatin gawar marigayin kana aka shugabanni suka bi sahu wajen gudanar da jawabansu inda da dama suka yi kalamai na girmamawa da kuma nuna irin sadaukar da kan da Helmut Kohl ya yi lokacin da ya ke shugabantar Jamus kana da irin gagarumar gudunmawar da ya bada wajen tabbatar da kafuwa kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Wannan ne ma ya sanya wasu ke ganin dalilin gudanar da taro na girmama shi a zauren majalisar dokokin kungiyar.

Trauerfeierlichkeiten für Altkanzler Kohl
Merkel ta jinjinawa Kohl bisa irin rawar da ya taka wajen hadewar Jamus waje gudaHoto: picture alliance/dpa/ M. Kappeler

Shugaban kungiyar EU Jean Claude-Juncker ya ce ''rasuwar Helmut Kohl rasuwa ce ta wani jarumi. Ya kafa tarihi sosai kuma sunansa zai kasance abinda ba za a manta da shi ba. Mutum ne da za a ce ya zama tamakar wani uba ko wani ginshi a wannan nahiya. Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus cikin rawar murya cewa ta yi ''ba don Helmut Kohl ba to da rayuwar jama'ar da ke kilace a bayan bangon Berlin ba ta sauya ba ciki kuwa har da tawa rayuwar. Ya kai shugaban gwamnati, gani a gabanka don yi maka godiya da game da damar da ka bani dakuma damar da ka baiwa al'ummar Jamus. Ina fatan wannan rasuwa taka ta kasance hutu gareka. Yanzu kam kalubale garemu shi ne mu dora daga inda ka tsaya.''

Speyer Trauerfeierlichkeiten für Altkanzler Kohl
An kewaya da gawar Kohl a mahaifarsa ta Ludwigshafen don bawa jama'a damar yin bankwana da shiHoto: picture-alliance/dpa/F. Kästle

To bayan da aka kammala wannan taro, an kuma dauki gawar tasa zuwa birnin Ludwigshafen da ke nan Jamus inda aka bi da ita ta tsakiyar garin don bada dama ga 'yan garin inda nan ce mahaifarsa su yi bankwana da shi kafin a kai shi kushewa. Bayan kammala zagayawa da shi a wannan birni da ke yammacin Jamus, an kuma dauki gawar wadda aka rufeta da tutar Jamus inda aka sanya ta jirgin ruwa da nufin don kaita garin Speyer idan nan ne aka tsara za a binne shi.

Da misalin karfe biyu da rabi na rana ne kuma gawar ta isa wannan birni da ke da muhimmancin gaske ga tsohon shugaban gwamnatin na Jamus inda aka kewaya da ita don jama'a su samu sukunin yi masa kallo na karshe tare yin bankwana da shi kana aka kaita majami'ar da ke wannan birni. To da misalin karfe shidda na yammaci inda baki kimanin 1,500 da aka gayyata ciki kuwa har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel suka hallara don yin addu'o'i da sauran abubuwa da suka kamata gannin binne tsohon shugaba.

Speyer Dom Trauerfeierlichkeiten für Altkanzler Kohl
Gabannin binne Helmut Kohl an gudanar da addu'o'i a majami'ar da ke Speyer kusa da mahaifar inda manyan baki suka halartaHoto: picture-alliance/dpa/M. Murat

Bayan kammala addu'o'i a wannan majami'a bisa jagorancin Bishop Karl-Heinz Wiesemann na darikar Katolika an binne Kohl a wata kushewa da ke daura da majami'ar sai dai ba duk jama'a ne suka halarci binne shi domin kuwa iyalinsa musamman ma maidakinsa da ya bari Maike Kohl-Richter sun bukaci kada a yi hakan, sabanin yadda aka saba gani ga shugabannin musamman ma dai a kasashen da wannan nahiyar.