1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar amfani da kyalen fuska ta fara aiki a Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou
April 27, 2020

Sannu a hankali Jamusawa sun kama hanyar cika wasu ka'idoji da hukumomin suka gindaya don yaki da yaduwar Corona ciki har da saka kyallen fuska da ya zama tilas a ciki motocin sufrin jama'a da shaguna.

https://p.dw.com/p/3bUSK
Deutschland Bayern | Frau mit Mundschutz
Hoto: picture-alliance/Sven Simon/F. Hoermann

A daukacin kasar dai ciki har da nan birnin Bonn an soma aiki da dokar a yau din nan , sai dai dokar na da dan sassauci a wasu yankunan musamman a birnin Berlin inda duk da tilasta wa jama'a saka kyalen a wuraren sufrin jama'a, abin ba haka ayake ba a shagunan sayen kayayaki.

Sannan rahotanni sun ce akwai matakin ladabtarwa ga wadanda suka gujewa aiwatar da dokar inda a Jihar Bayern hukumomi ke iya cin mutun tarar da ta kai kimanin euro 150.

Wannan dai wani ne daga cikin wasu muhimman matakan da hukumomin kasar suke dauka na sakin mara ga dokar takaita zirga-zirga, inda kawo yanzu wasu shagunan suka kasance a bude baya ga matakin bude wasu makarantu a farkon watan gobe.

Ya zuwa yanzu fiye da mutn 5. 750 ne suka rasa ransu daga cikin fiye da dubu 155  da suka kamu da Corona a nan Jamus.