1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar SPD a Jamus na taro kan batun 'yan cirani

Gazali Abdou Tasawa
July 4, 2018

Jam'iyyar SPD da ke kawancan mulki a Jamus za ta gudanar da taro domin bayyana matsayinta kan yarjejeniyar da CDU da CSU suka cimma kan batun 'yan cirani.

https://p.dw.com/p/30mV9
Deutschland Asylstreit - Koalitionstreffen im Kanzleramt | Andrea Nahles & Olaf Scholz, SPD
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Koall

Jam'iyyar SPD da ke kawancen masu mulki a nan Jamus ta sanar da amincewa a bisa manufa da yarjejeniyar da abokanan kawancanta na CDU da CSU suka cimma kan batun 'yan gudun hijira. Sai dai kuma ta ce za ta gudanar da taro tsakanin shugabanninta a wannan Laraba kafin bayyana matsayinta na karshe a kai.

 Amma dai shugaban jam'iyyar ta SPD kana mataimakin shugabar gwamnati Andrea Nahles ya bayyana cewa yana kyautata zaton samun fahimtar juna da abokanan kawancan nasu kan batun 'yan gudun hijirar. 

A jiya dai ne shugabannin jam'iyyun uku suka gudanar da taro a birnin Berlin domin cimma matsaya a tsakaninsu kan wannan batu na 'yan gudun hijira bayan da jam'iyyar ta SPD ta nuna shakkunta a game da yarjejeniyar da abokanan kawancan nata suka cimma a daren Litinin washe garin Talata wacce ta tanadi kafa wasu sansanonin karbar 'yan gudun hijira da kuma tantance su a kan iyakar kasar ta Jamus da makobciyarta ta Ostriya.