1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Likita ya kashe mutane sama da 100

Gazali Abdou Tasawa
November 9, 2017

Hukumomin shari'ar kasar Jamus na zargin wani likitan kasar da kashe mutane 106 wadanda ya yi jinyarsu a wasu gidajen asibiti biyu na kasar da ya yi aiki.

https://p.dw.com/p/2nM36
BG Deutsche Serienmörder | Krankenpfleger Niels H.
Hoto: picture alliance/dpa/C. Jasper

Hukumomin shari'ar kasar Jamus na zargin wani likitan kasar da kashe mutane 106. A cikin wata sanarwa da hukumomin shari'a da na 'yan sanda na birnin Oldenburg na Arewacin kasar suka fitar a wannan Alhamis, sun zargi likitan mai suna Niels Högel dan shekaru 41 da kisan mutanen da yake kula da lafiyarsu a gidajen assibiti guda biyu da yake aiki ta hanyar yi wa marasa lafiya alluran da suka wuce kima. 

Da ma dai tun a shekara ta 2015 kotun ta yanke wa wannan likita Niels Högel hukuncin zaman kason rai da rai bayan da ta sameshi da laifin kashe wasu mutanen biyu da ya yi jinyarsu. A karshen watan Agustan da ya gabata masu aikin binike sun zargi wannan likita da kashe akalla mutane 90 da yake kula da jinyarsu musamman wadanda ya lura na cikin halin raikwakwai mutu kwakwai. 

Yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutuwar wasu mutanen biyar a yayin da za a gudanar da aikin tono gawarwakin wasu mutanen a kasar Turkiya a ci gaban wannan bincike.