1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Merkel na ci gaba da fuskantar matsi

Abdourahamane Hassane RG
February 12, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta kare matakin da ake kallo a matsayin sakaci a yarjejeniyar kafa gwamnati bayan da ta bar mukamin ministan kudi ya subule wa jam'iyya mai mulki ta CDU.

https://p.dw.com/p/2sXgh
Deutschland Sommerinterview im ZDF mit Angela Merkel
Hoto: picture alliance/dpa/ZDF/J. Detmers

Angela Merkel  ta yi tsokaci kan batun ne a yayin wata hira da aka yi da ita a gidan talabijan na ZDF na Jamus da ke Berlin babban birnin kasar a game da kawancen da jam'iyyar ta kula da jam'iyyar SPD a makon jiya wanda 'yan jam'iyyarta na CDU suka bayyana takaicinsu da kuma yin da na sani a game da kawance.

Jam'iyyar ta 'yan mazan jiya watau CDU na zargin shugabar da yin sakaci a yarjejeniyar bayan da ta sallama matsayin ministan kudi da ta bai wa 'yan jamiyyar SPD wanda tsawon shekaru takwas ya ke a cikin hannu  jam'iyyar ta CDU. Shin anya ba ki yi muguwar tattaunawa ba wacce aka kwari jam'iyyarki? Tambayar farko  da 'yar jaridar gidan talabijan na ZDF Bettina Schausten ta yi wa Angela Merkel kenan a tattaunawar da suka yi.

Merkel dai ta amsa da cewa tana cike da farin ciki dama aka iya kai wa ga cimma yarjejeniyar tana mai cewa. ''Da farko na yi murna da muka cimma wannan yarjejeniya ta kawance wacce a wurinmu, daidai ya ke da bukatun mu, mun tattauna abubuwa da dama tare da SPD wacce ta sa rai sossai a kan wasu mukaman.

Martin Schulz wanda yarjejeniyar ta amince a matsayin ministan kudi
Martin Schulz wanda yarjejeniyar ta amince a matsayin ministan kudiHoto: picture alliance/dpa/K.-D. Gabbert

Rashin samun matsayin ministan kudi da ya kubucewa jam'iyyar ta CDU, ya janyo wa Merkel bakin jini a idon ya'yan jam'iyyarta, don  wasu masu adawa da ita na cewa magoya bayan jam'iyyar da dama ne za su fice zuwa jam'iyyar masu tsatsaura ra'ayi a sakamakon wannan mataki. Amman Merkel ta ce duk da haka ba su da zabi face yin hakan.''Ta ce da ciwo a game da yadda muka rasa mukamin ministan kudi, amma a gani na za mu iya amincewa da haka domin shi ne mafita. Da dai abin da ya kamata mu gayawa jamaa shi ne irin abin da yarjejeniyar kawacen ta kunsa ba wai magana ba ce ta rabon mukamai, a gareni hakan ba daidai ba ne.

Koalitionsverhandlungen von Union und SPD
Merkel za ta ci gaba da shugabancin Jamus har cikan wa'adin mulki na shekaru huduHoto: picture-alliance/dpa/G. Fischer

Duk da irin matsin da ta ke fuskanta daga magoya bayan jam'iyyar CDU Angela Merkel ta dage wajen cika wa'adin mulkinta na shekaru hudu. Yarjejeniyar kawancen da CDU ta cimma da SPD nan gaba ne a babban taron Congres, jam'iyyar ta CDU za ta tantance shi a taron da ake ganin yana cike da kalubale ganin matsalar da ake fuskanta na rarrabuwar kawuna. Yayin da kuma 'yan jam'iyyar SPD  za su sake kada kuri'ar raba gardama a kan yarjejeniyar  a cikin watan maris da ke tafe.