1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Merkel ta tabbatar da shirin kafa kawance

Gazali Abdou Tasawa
October 7, 2017

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a hukumance a wannan Asabar aniyarta ta soma tattaunawa da jam'iyyar FDP da kuma ta The Greens domin kulla sabon kawancan da zai kafa gwamnati.

https://p.dw.com/p/2lQZI
Deutschland Dresden Deutschlandtag der Jungen Union Angela Merkel
Angela Merkel a taron matasan jam'iyyarta ta CDU a birnin DresdenHoto: picture-alliance/dpa/M. Skolimowska

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a hukumance aniyarta ta soma tattaunawa da da jam'iyyar FDP da kuma ta The Greens domin kulla sabon kawancan da zai kafa gwamnati. 

Merkel ta bayyana wannan aniya tata ce a lokacin wani jawabi da ta gabatar a gaban matasan jam'iyyar CDU a birnin Dresden na gabashin kasar. A zaben majalisar dokoki na ranar 24 ga watan Satumba jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta CDU ta Angela Merkel ta samu kashi 33 cikin 100, ta masu sassaucin ra'ayi ta FDP na da kashi 10,7 cikin 100, a yayin da ta The Greens ta tashi da kashi 8,9 cikin 100.

Idan dai har wannan kawance ya tabbata to kuwa wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar ta Jamus da gambizar da ake yi wa lakabin "Kawancan Jamaika" da ke hada masu ra'ayin mazan jiya da masu sassaucin ra'ayi da masu kare muhalli za su yi mulki a tare a kasar ta Jamus.