1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na ɗaukar matakai a kan Ebola

August 13, 2014

Hukumomin ƙasar sun gargaɗi 'yan ƙasarsu da su fice daga Saliyo da Liberia da kuma Guinea sakamakon yadda cutar ke ƙara yaɗuwa a yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1CtX8
Hoto: Reuters/Samaritan's Purse

Ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan ƙarin jama'ar da ake samu da ke mutuwa waɗanda suka kamu da cutar ta Ebola a cikin ƙasashen yankin na yammancin Afirka.

Wani kakakin ofishin ministan harkokin waje na ƙasar ta Jamus Martin Schäfer; ya ce kiran bai shafi jami'an kiwon lafiya ba, da masu aiki agaji da ke ba da tallafin gaggawa , sannan ya ce ofishin jakadancin Jamus ɗin zai ci gaba da kasancewa a buɗe a cikin ƙasashen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu