1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na karbar bakuncin shugabanni kan rikicin Ukraine

October 19, 2016

Duk da cewa ci gaban da aka samu a Gabashin na Ukraine daga dukkanin bangarorin biyu ba wani abin kirki ba ne Shugabar gwamnati Merkel ta ce za ta yi amfani da wannan dama.

https://p.dw.com/p/2RQKi
Russland Merkel und Putin
Hoto: imago/ZUMA Press

A ranar Laraban nan ce Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke karbar bakuncin shugabanni daga kasashen Rasha da Ukraine da Faransa , taron da ke da buri na ganin an sake farfado da battun yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a yankin Gabashin na Ukraine. Sannan a na ganin yayin taron za a kuma tattauna kan rikicin Siriya.

Duk da cewa ci gaban da aka samu daga dukkanin bangarorin biyu ba wani abin kirki ba ne Shugabar gwamnati Merkel ta ce za ta yi amfani da wannan dama wajen ganin an samu ci gaba mai ma'ana.

Sama da shekara guda dai kenan kafin a sake ganin Shugabar gwamnati Merkel da Shugaba Vladimir Putin na Rasha da  Francois Hollande na Faransa.