1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na shirin kafa dokar hana saka nukabi

Gazali Abdou TasawaAugust 19, 2016

Ministan cikin gidan na Jamus Thomas de Maiziere ne ya bayyana hakan a karshen wani taro da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta shirya a wannan Jumma'a tare da sauran jam'iyyu abokanin kawancanta.

https://p.dw.com/p/1Jlld
Symbolbild Frauentag
Hoto: picture-alliance/dpa/Arshad Arbab

Kasar Jamus na shirin daukar matakin haramta saka tufafin burka da nikabi a wasu guraren taruwar jama'a a kasar. Ministan cikin gidan kasar Thomas De Maiziere ne ya bayyana hakan a karshen wani taro da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta shirya a wannan Jumma'a tare da sauran jam'iyyu abokanin kawancanta.

Wannan mataki da jam'iyyun suka ce za su shigar da bukatar mayar da shi a matsayin doka a wani mataki na kyautata tsaro a kasar zai tanadi haramta saka nikabi da duk wata tufa mai rufe huska a ma'aikatun gwamnati da makarantu da jami'o'i dama a cikin kotuna da sauran guraren taruwar jama'a ko kuma a lokacin tukin mota.

Sai dai ministan bai bayyana wani jadawali na lokacin da za su shigar da wanann doka ba wacce tuni ta fara fuskantar adawa har a bangaren masu ra'ayin mazan jiya ta SPD mai kawance da jam'iyar CDU ta firaminista Angela Merkel.

Tufafin nikabi da burka dai na neman zaman ruwan dare a kasar ta Jamus tun bayan da ta bayar da mafaka da 'yamn gudun hijira sama da miliyan daya kasashen Siriya da Iraki.