1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Afirka a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
November 8, 2019

Batun rufe kan iyakokinta da Tarayyar Najeriya ta yi da kuma batun yaki da Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun dauki hankulan jaridun Jamu na wannan makon.

https://p.dw.com/p/3Si6E
Nigeria Seme Grenze zu Benin
Tsakamai wuya sakamakon rufe kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin, Hoto: Reuters/A. Sotunde

Zamu shirin da labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta mai taken "Matakin yaki da 'yan simoga ya jefa Jamhuriyar Benin cin tsaka mai wuya".

Jaridar ta ci gaba da cewar Najeriya da ke da yawan al'umma a nahiyar Afirka, ta rufe kan iyakokinta domin hana shigo da kayayyaki kasar ba bisa ka'ida ba, sai dai hakan ya jefa Benin da ke makwabtaka cikin mawuyacin hali.

Semeborder kamar yadda ake kiran mashigin da ke tsakanin kasashen biyu dai, na daya daga cikin manyan wuraren hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka. Daruruwan manyan motoci ne ke ketarewa ta wannan hanyan a kowacce rana, a yayin da dubban 'yan kasuwa ke safarar kayayyakinsu cikin kananan motoci ta wannan hanyar. Masu hada-hadar canji daga bangarorin kasashen biyu na cin gajiyar wannan shige da fice da ke gudana.

Sai dai duk wannan ya tsaya cak sama da watanni biyu da suka gabata. A ranar 20 ga watan Augusta ne dai  Najeriyar ta sanar da rufe kan iyakonkinta da sauran makwabtanta na kasashen yammacin Afirka tare da haramta safarar kayayyaki zuwa cikin kasar.

Kasashen Nijar da Chadi da Kamaru suma sun shiga cikin mawuyacin haliN, amma Jamhuriyar Benin ta fi zama cikin ukuba, kasancewar tashar jiragen ruwa da ke Kotono, na zama babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci da shigo da kayayyaki.
Ita kuwa jaridar die tageszeitung sharhi ta rubuta game da halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango mai taken" Raguwar cutar Ebola, karuwar yake-yake". Jaridar ta ce, a yanzu haka cutar Ebola ta fara kauracewa zuwa Ituri da ke yankin arewa maso  gabashin kasar, inda ake hakar ma'adanin tagulla.

BG Ebola-Ausbruch im Kongo
Bincike kan Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Hukumar kula da lafiya ta duniya wato WHO, ta yi farin cikin sanar da cewar mutane 10 ne kacal suka kamu da cutar ta Ebola tsakanin makon karshe na watan Oktoba zuwa farko watan Nuwamba a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Yanzu haka dai a cewar hukumar babu barazanar yaduwar wannan muguwar cuta zuwa kasashen Yuganda da Ruwanda da ke makbtaka, sai dai fargabar ita ce yadda yaduwar cutar ke kaurace daga gundumar Kivu zuwa Ituri da ke arewaci, musamman saboda karancin kayayyakin more rayuwa da ma jami'an agaji a wannan yankin.

Kungiyoyi agaji na kokawa kan yadda jama'a suke ci gaba da yin gudun hijira a yankin na gabashin Kwango sakamakon karuwar fada tsakanin mayakan sa-kai da dakarun gwamnati.

Äthiopien neue Lebensmittel Lieferservice
Fari: Mutane da dabbobi na cikin tsaka mai wuya a kudancin AfirkaHoto: DW/J. Jeffrey

Ita kuwa Jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi dangane da fari a yankin kudancin Afirka. Jaridar ta ce yanayin karancin ruwan sama a yankin Kudancin Afirka babbar barazanace ga rayuwar dan Adam da dabbobi.

"Victoria falls" inda ruwa ke kwararowa daga cikin duwatsu, wanda ke zama daya daga cikin wuraren al'ajabi na duniya, ya fara bushewa. A baya dai kana iya hangen ruwan daga nisan kilomita 30, sabanin yanzu.

Yankin kudancin Afirka mai kasashe 16, na fuskantar mafi munin fari a karon farko sama da shekaru 35. A cewar Margaret Malu da hukumar samar da abinci ta duniya, kimanin mutane miliyan 45 ne suke fuskantar barazanar yunwa cikin watanni shida masu zuwa, annobar da ke zama irinta na farko a tarihi.