1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta dauki kofin duniya

July 14, 2014

A wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya Jamus ta doke Argentina, abinda ya bata nasarar daukar kofin. Kasar ta kuma dauki kofin duniya karo na hudu a tarihinsa.

https://p.dw.com/p/1CcLc
Fußball WM 2014 Brasilien Deutsche Fußballnationalmannschaft Jubel Pokal
Hoto: Reuters

Dan wasanta Mario Götze ne ya zura kwallo a ragar Argentina bayan da aka dawo zagaye na biyu na karin lokaci. Jamus dai rabonta da ta ci gasar kofin duniya tun 1990 lokacin da ta doke Argentina a birnin Rom na kasar Italiya.

To dama dai a kan ce wai mahakurci, mawadaci.

Bayan hakurin jira na tsawon shekaru 24, Jamus, a karo na hudu ta zama zakaran duniya a fagen wasan kwallon kafa. Bayan wasanni na tsawon makonni hudu, ranar Lahadi a birnin Rio de Jeneiro, kuma cikin gagarumin filin wasan nan mai dadadden tarihi, wato Maracana, Jamus ta shiga wasan karshe tsakaninta da Argentina. Wasan na ranar Lahadi kuma shine na uku na karshe a jerin wasannin cin kofin duniya tsakanin kasashen biyu, inda ko wacce ta sami nasara sau daya. To sai dai a wasan da ya gudana a ranar Lahadin, Jamus ta sami nasara da ci daya ba ko daya, ko da shike sai da aka yi kare jini, biri jini, inda bayan minti 90 babu inda aka ci, kasashen biyu suka sami karin minti 30. A tsakanin wannan lokaci na kari ne, dan wasan Jamus mai suna Mario Götze, wanda ma daga baya aka shigar da shi a wasan, yayi wa dimbin magoya bayan Argentina da ke filin wasan da kuma masu kallonsu a can gida sakiyar da ba ruwa, inda misalin minti 113 da fara wasan, ko kuma bayan an shiga minti 23 na karin lokaci, ya jefa kwallo a gidan yan wasan Argentina, wato misalin sauran minti bakwai kenan a tashi wasan gaba daya.

Fußball WM 2014 Finale Argentinien Deutschland
Mario GötzeHoto: Reuters

Tun kafin a shiga wasan karshen a ranar Lahadi, sai da Jamus ta yi wasanni bakwai, inda daga ciki ta yi kunnen doki daya ne kawai a karawa tsakaninta da Ghana tun a zagayen farko. Jim kadan kafin wasan na karshe, mai koyar da 'yan wasan Jamus, Joachim Löw ya ce Jamus tana mutunta wasan Argentina, amma ba za ta shiga filin da tsoro ba, saboda ya san cewar ko wacce daga cikinsu, za ta fito ne da karfinta, kuma za ta yi wasa sai inda karfinta ya kare. A karshen wasan Löw ya ce dama ya san haka wasan zai gudana, babu kasar da za ta kyale 'yar uwarta ta sha ruwa.

"Dama can mun san cewar 'yan Argentina za su tattara karfinsu gaba daya, a irin wannan wasa na karshe. Nasarar da muka samu ba ta zo mana da sauki ba, saboda 'yan wasanmu, sun yi kokarin da ya wuce kima, sun yi abin da ba a zato. A yau duk abin da suka iya sun ba da shi a filin wasa fiye da yadda na taba gani domin su cimma burin da ba su taba sanya hankalinsu a kansa kamar a wannan karo ba, wato su dauki wannan kofi su koma da shi gida".

A karshe Jamus ta kai ga daukar kofin na duniya da ci daya ba ko daya kan Argentina. Hakan ya bai wa Jamus damar daukar kofin karo na hudu, bayan shekara ta 1954 da 1974 da 1990, kuma ta zama kasa ta biyu bayan Brazil a jerin kasashen da suka fi daukar kofin na duniya. Dangane da wannan kwazo, Captain na 'yan wasan Jamus, Philipp Lahm ya ce:

Fußball WM 2014 Brasilien Deutsche Fußballnationalmannschaft Jubel Pokal
Hoto: Reuters

"Abin mamaki ne irin kokarin da muka nuna yau tsawon minti 120, inda a karshe muka cimma burinmu. Irin wannan haline ya sanya muka yi fice tsakanin sauran kasashe. Bamu damu da ace kowa cikinmu gwani bane, abin da ya fi mana muhimmanci shi ne mu hada karfinmu wuri guda kamar yadda muka yi yau da kuma tsawon wadannan wasanni".

Cikin shugabannin kasar da suka shaidar da wasan na ranar Lahadi a birnin Rio de Jeneiro, a jerin manyan baki har da shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel da shugaban kasa, Joachim Gauck, wanda ma daga baya ya ce 'yan wasan Jamus sun yi rawar gani, kuma ita kanta hukumar kwallon kafar Jamus, wato DFB wajibi ne a yaba mata.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal