1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan cinikin makamai da Saudiyya

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2019

Gwamnatin Jamus ta za ta dau watanni shida ba tare da sayarwa Saudiyya makamai ba saboda zargin kisan fitaccen dan jarida Jamal Khashoggi a Turkiyya.

https://p.dw.com/p/3FrSk
Deutschland Waffenproduktion & Waffenexport | Heckler & Koch - Messe in Paris, Frankreich
Hoto: Getty Images/AFP/G. Julien

Matakin na Jamus ya fuskanci kakkausar suka daga ciki da wajen kasar, inda kawancen kasashen Kungiyar Tarayyar Turai kamar Birtaniya da Faransa ke ganin matakin zai shafi ayyukan tsaro na hadin gwiwa.

Kungiyoyin kare hakkin fararen hula sun yi maraba da matsayar Jamus na daina fitar da manyan makaman yaki da sunan ciniki zuwa Saudiyya da ma sauran kasashen da ake zargi da hannu a yakin Yemen.