1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus tace mai yiwu´wa ne ta horasda sojojin Iraqi

December 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuYS

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel tace mai yiwune kasar jamus ta taimaka wajen horasda sojojin Iraqi a wajen Iraqin,bayan kiraye kiraye da akayi ga gwamnatocin kasashen turai dasu kara taimakawa wajen kawo zaman lafiya a kasar ta Iraqi.

Merkel ta fadawa taron manema labari bayan ganawarta da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak cewa,duk da cewa har yanzu babu wani takamammen shiri na horasda sojin na Iraqi,jamiai daga maaikatar harkokin tsaro ta jamus suna tattaunawa da takwarorinsu na Iraqin.

Tun farko ministan harkokin wajen Jamus Frank Welter Steinemeire dan jamiyar SPD yayi watsi da kira da jamiyar Merkel da kuma jakadan Amurka a Berlin sukayi na cewa ya kamata Jamus ta kara bada taimakonta ga Iraqi.

Steinemeire yace tuni dai Jamus ta bada nata taimako a bangaren rage basukan dake kann Iraqi tare da horasda yan sandanta da kuma taimakawa ga sake gina kasar.