1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta karawa Somaliya tallafi

Abdul-raheem Hassan
May 1, 2017

Gwamantin Jamus za ta rubanya kudaden agaji da za ta baiwa Somaliya dan yakar matsalar fari da yunwa da ke addabar al'ummar kasar kimanin miliyan biyar.

https://p.dw.com/p/2cCDH
Außenminister Gabriel besucht Somalia
Hoto: picture alliance/dpa/M.Gambarini

Ministan harkokin wajen Jamus Sigma Gabriel ya tabbatar da wannan alkawari a wata ziyarar ba zata da ya kai Magadishu babban birnin kasar. A baya dai Jamus ta yi alkawarin baiwa Somaliya kudin euro dubu 70. Ministan harkokin wajen na Jamus ya ce a yanzu kasar za ta samar da miliyan 140 na kudin euro da nufin karfafawa Somaliya guiwa don cimma burinta na 'yanta kasar daga bala'in fari da ya jefata cikin rashin abinci.

Firaiministan Somaliya Hassan Ali Khaire ya ce sun yaba da irin hobbasa na jinkai da kasar Jamus ke nunawa kasahen da ke fama da matsalar fari musamman a Afirka, inda ya ce kudaden za su taka rawar gani wajen sharewa 'yan kasar hawaye. Kasashen Somaliya da Sudan ta Kudu da Yemen da kuma arewacin Najeriya na cikin kasashe da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana neman taimakon kudi dalar Amirka biliyan hudu da rabi tun watan Afirilu na shekara ta 2016 don su tsira daga kangin rashin abinci da ke addabar su sanadiyar bala'in fari da rikice-rikice.