1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta zurfafa bincike kan Amirka

November 7, 2013

Kwamitin majalisar dokokin Jamus na shirin ganawa da Edward Snowden kan satar sauraron wayar shugabar gwamnati Angela Merkel.

https://p.dw.com/p/1ADPj
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani kwamitin majalisar dokokin kasar Jamus, ya ce zai yi kokarin tambayoyi wa tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka, Edward Snowden a Rasha.

Kwamitin zai duba hanyoyin da Amirka ta bi, wajen satar sauraron wayar Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel. Tambayoyin za su shafi abubuwan da aka bankado na satar sauraron wayoyi daga tsohon jami'in hukumar leken asirin kasar ta Amirka. Snowden ya samu mafaka na wani lokaci a Rasha.

Tuni jam'iyyun adawa na kasar Jamus suka nemi a ba shi mafakar a wannan kasa, saboda ya samu damar zuwa ya yi bayani a kan hakikanin abin da ya faru.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar