1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janyewar dakarun 'yan awaren Ukraine

Pinado Abdu WabaFebruary 24, 2015

Dakarun 'yan awaren Ukraine sun ce sun fara janyewa bisa tanadin yarjejeniyar sulhu, sai dai har yanzu ana tababan sahihancin wannan labarin.

https://p.dw.com/p/1EgXl
Kämpfe in der Ostukraine 02.02.2015 Prorussische Seperatisten
Hoto: D. Faget/AFP/Getty Images

Dakarun awaren Rasha a yankin gabashin Ukraine sun ce sun fara janye makamansu bisa tanadin yarjejeniyar sulhun kasa da kasa da ke da burin samar da tazara tsakanin 'yan awaren da makaman attileryn dakarun Ukraine.

Sai dai kamfanin dillancin labaran AFP na Faransa ya ce ba a kai ga tantance kalaman na Eduard Basurin ba, daya daga cikin manyan hafsoshin 'yan tawayen, a yayinda shi kuma mai magana da yawun tawagar da ke sanya ido kan yadda lamura ke gudana a kasar Michael Bociurkiw ya ce ba zai iya mayar da martani ba har sai ya sami rahoto da yammacin yau.